1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar siyasar Angela Merkel

May 13, 2012

Zaben majalisar jihar North Rhein Westphalia zai aike muhimmin sako ga fadar gwamnatin Jamus da ke birnin Berlin

https://p.dw.com/p/14trO
Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) spricht am Montag (16.04.2012) beim Empfang zum dritten Jugendintegrationsgipfel im Bundeskanzleramt in Berlin zu den Teilnehmern. Der Jugendintegrationsgipfel dient als Ideenschmiede, wie die Integration weiter voran gebracht werden kann. Foto: Kay Nietfeld dpa
Bundeskanzlerin Angela Merkel beim Jugendintegrationsgipfel 16.04.2012Hoto: picture-alliance/dpa

A ranar Lahadi, 13.05.2012 ne ake gudanar da zaben majalisar jihar North Rhein Westphalia(NRW) ta kasar Jamus, wadda mutane miliyan 18 da ke zaune cikinta ke fatan ganin ingancin tattalin arziki. Ko shakka babu wannan zabe, zabe ne da zai yi tasirin gaske ga makomar gwamnatin Angela Merkel, da ke jan ragamar shugabancin kasar a halin yanzu.

Dan takarar jam'iyyar da ke mulkin Jamus

Ita dai Angela Merkel ta ba da goyon bayanta ga Norbert Roettgen da zai tsaya a karkashin tutar jam'iyyarta ta CDU a zaben na jihar North Rhein Westphalia. To sai dai wannan goyon baya babu abin da zai tabuka wa dan takarar, wanda tuni ya shafe makonni yana fuskantar zolaya daga masu adawa da shi. Shi dai Norbert Roettgen kasancewar an dade da gano gurinsu na zama wanda zai gaji Merkel, babu wani tagomashi da zai samu a zabukan yankunan Rhein da Ruhr da ke da muhimmaci a jihar. Kuma ko da yake zai iya karfafa ikon da yake da shi a jam'iyyarsa idan an zabe shi, to amma da wuya ya samar da sauyi a ofishin gwamnar jihar da ke birnin Duesseldorf. Ko da yake shi kansa ba ya fitowa fili ya fadi hakan, to amma jam'iyyarsa ta fahimci lamarin. Tun sosomin kamfen Roettgen na yakin neman zabe ne dai, masana suka bayyanar da shi a matsayin wanda zai sha kayi a zaben. Ga dai abin da shi kansa ke cewa:

Alamar jahar NRW
Wahl in NRWHoto: picture alliance / dpa

"Ni dai a ko da yaushe ina mai ra'ayin cewa za a iya samun sauyin gwamnati a inda majalisa ke kunshe da bangarorin biyar. To amma abin takaici sai ga shi kuma mun kafa gwamnati ta marasa rinjaye tare da jam'iyyar die Linke(mai ra'ayin gurguzu). A hakika ni ba zan so daukar irin wannan mataki ba."

Hasashe kan sakamakon zaben

Tuni ne dai sakamakon kuri'un jin ra'ayi suka bayyanar da cewa Roettgen ba zai samu kuri'u masu yawan a zo a gani ba a zaben. Hakan dai na ma'anar cewa nan ba da jimawa ba Merkel da jam'iyyarta ta CDU za su yi kasa a gwiwa. To sai dai shugabar ta gwamnatin Jamus ta kau da tsoro a zukatan 'ya'yan jam'iyyarta inda take cewa:

+++Bild alternativ geschnitten:+++ Foto vom 7.5.2012: NRW-Ministerpräsidentin und SPD-Spitzenkandidatin Hannelore Kraft im Wahlkampf, hier in Dülmen im Norden von Nordrhein-Westfalen mit einer Frau, die ihr viel Glück für den Wahltag wünscht Foto: DW/Andrea Grunau
Hannalore Kraft (dama) a yakin neman zabeHoto: DW

"Kada ku razana game da yiwuwar yin gamin gambiza a zaben majalisun jihohi. Tuni na tsai da shawarar kin yin hakan."

Ko shakka babu rawar da jam'iyyar SPD za ta taka a wannan zabe zai iya aike sako ga fadar gwammnati da ke a birnin Berlin kasancewar sakamakon kuri'un jin ra'ayi ya bayyanar da samun nasarar jam'iyyar SPD akan CDU. Hannelore Kraft, gwamnar jihar North-Rhein Westphalia ta jam'iyyar SPD ita ce ke kan gaba idan aka kwatanta da Roettgen- abin da zai kawo sauyin rawar da SPD ke takawa a birnin Berlin. Hannelore Kraft ta ce:

Tasirin zaben kan fadar gwamnati da ke Berlin

"Tuni hakan ya aike sako ga fadar gwammnati da ke a birnin Berlin. A bayyane yake cewa SPD ita ce ke kan gaba a sakamakon kuri'ar jin ra'ayi. Hakan na nuni da kasancewarmu a tsaka tsakiyar hanyar samun daukaka a can Berlin fiye da ma nan jihar NRW. Mun yi aiki sosai tare da taka rawar gani wajen kafa gwamnatin marasa rinjaye a nan jihar. Kuma matakin yin hakan shi ne zai mana jagora zuwa birnin Berlin."

Bundeskanzlerin Angela Merkel und NRW Landespolitiker Norbert Röttgen auf der Bühne zusammen. Fr. Merkel war beim Besuch in Bonn, hat NRW Landespolitiker Norbert Röttgen unterstützt 20 Tage vor der Wahl am 13. Mai; 23.04.12, auf dem Markt vor dem Bonner Rathaus; Copyright: DW/Diana Fong (englische Redaktion)
Merkel da Roettgen a yakin neman zabeHoto: DW

A baya ga wadannan 'yan takara biyu akwai Christian Lindner, wanda zai tsaya da tutar jam'iyyar FDP da ke gamin gambiza da jam'iyyar Merkel. To ko shin wannan jam'iyya za ta iya karfafa gwiwar gwamnatin ta gamin gambiza a Berlin? Wallahu a'alamu. Sai kuma jam'iyyar Pirates wanda a cikin dan kankanin lokaci bayan girkuwarta ta iya ta samu magoya baya da dama.

Daga kasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto.

Mawallafi: Volker Wagener/Halima Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu / US