Makomar shari'ar wasu 'yan Amurka a Masar
March 1, 2012Mahukuntan Masar sun cire takunkumin hana zirga-zirgar da suka sayanwa wasu 'yan Amurka guda bakwai, wadanda ake tuhuma da haddasa tarzoma a yayin da suke aiki da wasu kungiyoyi masu rajin kare demokradiyya, wadanda kuma ke samun tallafi ta haramtattun hanyoyi. Wannan mataki dai na nuna alamar kawo karshen rikicin diplomasiyya mafi muni a dangantakar da ke tsakanin kasashen Masar da Amurka na tsawon shekaru 30 yanzu. A jiya laraba ne lauyan da ke kare 'ma'aikatan kungiyoyin ya ce 'yan Amurkan bakwai a ciki har da dan shugaban hukumar sufurin Amurkan Ray Lahood zasu iya barin kasar ne kadai idan suka biya milliyan biyu na kudin Masar, sa'an nan sun kuma sanya hannu kan cewa zasu cigaba da kasancewa a shariar tasu. Ana tuhumar wadannan mutane da amfani da kudaden da suka samu ta haramtattun hanyoyi wajen harzuka mutane su yi adawa da shugabanin sojin kasar. Ba'a riga an san ko za'a wanke 'yan Amurkan daga wannan zargi ba.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Umaru Aliyu