Makomar rikicin Siriya
February 24, 2012Shugabanin Larabawa a wannan juma'ar sun yi kira da a aika da wata tawagar masu wanzar da zaman lafiya zuwa Siriya, a wani taron da aka kaddamar da zuman matsawa gwamnatin Damascus da ta dakatar da zud da jinin da ke gudana, ta kuma bar ma'aikatan agaji su kai tallafi ga inda ake bida. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Mrs Hillary Clinton, ta ce shugaba Basahr Al Assad zai fuskanci hukunci mai tsauri sakamakon rashin kulawa da kiraye-kirayen da alummar kasa da kasa ta yi ta masa na ya daina murkushe 'yan adawa. Haka nan kuma ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe, ya kwatanta majalisar 'yan adawan Siriyar ta SNC a matsayin halastacciyar gwamntin kasar.
Akalla mutane 22 suka hallaka ko bayan da kasashen larabawa da na yamma suka fara gudanar da taro a Tunisia, taron da suka yi wa take "taron kolin kawayen Siriya" wanda ke da burin aikawa gamnatin Assad da kakkarfar sako.
Wannan taro yana zuwa ne wuni biyu kafin a kira alummar Siriyar zuwa jefa kuri'a kan sabon kundin tsarin mulkin da zai kawo karshen mulkin jamiyyar Baath duk da cewa zai barwa shugaban kasa mafi yawan iko.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi