1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Euro-Gruppe Brüssel

March 13, 2012

Rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin euro sun amince su baiwa Girka kaso na biyu na kudin da aka alakawarta mata domin tayar da komadar tattalin arziki

https://p.dw.com/p/14K6M
Source News Feed: EMEA Picture Service, Germany Picture Service (L to R) Greece's Prime Minister Lucas Papademos, Finland's Finance Minister Jutta Urpilainen, Germany's Finance Minister Wolfgang Schaeuble and Dutch Finance Minister Jan Kees de Jager attend a Eurogroup meeting at the European Union council headquarters in Brussels February 20, 2012. Euro zone finance ministers are expected to approve a second rescue package for Greece at a meeting on Monday, a move officials hope will draw a line under four months of social unrest and financial market turmoil that has shaken Athens. REUTERS/Yves Herman (BELGIUM - Tags: BUSINESS POLITICS)
Hoto: Reuters

Ministocin kuɗi na ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗi ta Euro sun amince su bai wa Girka kaso na biyu na kudin da ta ke bukata domin tayar da komaɗar tattalin arzikinta.

A Lokacin wani taro da suke gudanarwa a birnin Brussels na Beljium, ministocin sun yi alkawarin duƙufa kan wani sabon rikicin kudi da ya kunno kai a spain domin neman warware shi.

Su dai ministocin na kuɗi sun kusan zuba ruwa a ƙasa su sha, saboda murnar kashe gobarar kuɗi da ta yi barazanar tasowa a Girka da suka yi. Da ma dai tun lokacin da ya iso zauren taron na birnin Brussels shugaban rukunin ƙasashen da ke amfani da Euro wato Jean claude Junker, ya bayar da tabbacin cewar haƙar Girka ta samun tallafi ta kama hanyar cimma ruwa.

"Ko Shakka babu, za mu yi na'am da shirin tallafa wa Girka da kuɗi da za a ƙaddamar."

Ranar laraba 14 ga watan maris ne ƙasashen na Turai za su sa hannu akan takardar da za ta bayar da damar sakar wa Girka miliyon dubu 130 na Euro da ta ke bukata.

Source News Feed: EMEA Picture Service, Germany Picture Service Greece's Prime Minister Lucas Papademos (L), Germany's Finance Minister Wolfgang Schaeuble (2nd L) and Netherland's Finance Minister Jan Kees de Jager (3rd L) speak to each other during a Eurogroup meeting at the European Union council headquarters in Brussels, in this February 20, 2012 file photo. In interviews with dozens of players involved in the seven months of talks among banks, national governments, the European Union, European Central Bank and International Monetary Fund, Reuters has pieced together how the agreement - Greece's second bailout - came together and how close it came to failing. To match Insight EUROPE-GREECE/ REUTERS/Yves Herman/Files (BELGIUM - Tags: BUSINESS POLITICS)
Hoto: Reuters

Ita dai wannan ƙasa ta ci wannan gajiya na kudi ne, sakamakon musaya da ta yi da kanfanoni masu zaman kansu, wadda ta bata damar rage miliyon dubu 100 na gammon bashin da ke neman yi wa gwamnati katutu. Rawar da masana'antun na Girka suka taka, zai bata damar rage giɓin da ta samu a fiskar bunƙasar tattalin arziki da kashi 117 cikin 100 kafin nan da shekara ta 2020, maimakon giɓin kashi 160 daga cikin 100 da ta yi fama da shi a baya.

Ministan kudin Girka, Evangelos Venizelos, ya ce wannan mataki na haɗin guiwa da suka ɗauka, wani abin alfahari ne.

"Ina sa ran cewar za a ci gaba da samun gudunmwa daga kanfanoni masu zaman kasu. Yanzu dai abin da muka sa a gaba, shi ne aiwatar da abubuwan da muka yi alkawari, wadanda kuma za su bamu damar samun bunƙasar tattalin arziki a Girka."

Tanadin ƙasashen Turai kan wadanda ke fama da karayar arziki

Sai dai kuma tun kafin a kai ga cimma wannan tudun na tsirar a Girka, ɗaya daga cikin mambobin Eurogroup wadda ba wata ba ce illa spain ta shiga cikin wannan tasku na matsin arziki. Tuni dai a shekarar da ta gabata ne hukumomin Madrid suka samu gibin kashi 8 da digo biyar na bunkasar tattalin arziki.

Duk kuma da jan kunne da takwarorinsu na Turai suka yi musu, a bana ma shugabanni na Spain sun yi hasashen sake samun gibi na kashi 5 da digo 8 maimakon kashi 4 da digo 4 kamar yadda aka gindaya musu.

Sai dai kuma komishinan EU da ke kula da harkokin kuɗi wato Olli Rehn ya bayyana lokacin wani taron manaima labarai cewar har yanzu sassa da ke tafiyar da kungiyar EU, ba su tsayar da sahihiyar hanyar tsamo tattalin arzikin spain din daga dakushewa ba. saboda haka ne ministar kudi ta Austria Maria Fekter ta gargadi Spain da ɗaukan matakan tsumi da suka wajaba domin fita daga wannan ƙangi.

"Dole ne Spain ta yi aiki tukuru domin tayar da komadar tattalin arzikinta. matakin farko da ya kamata ta dauka shi ne ta dauka sharudan da za'a gindaya mata da mahimmaci, kana ta nemi cike kowanne daga cikinsu.

Tuni dai gwamnatin Frime minista Rajoy ta ce za ta yi iya kokarinta domin ganin cewa ta rage wannan koma bayan da ta ke fiskanta a cikin shekara mai kamawa. Dama dai dokokin bankin ko ta kwana da kasashen da ke amfani da Euro suka kafa, sun tanadi ladabtar da duk ƙasashe kamar spain da suka gaza samun bunkasa na kashi 3 daga cikin 100, kana suka kasa rage bashin da ya kai musu iya wuya.

Mawallafi: Mohammed Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar