Makarantar koyar da ilimi kyauta a Ghana
October 19, 2016
Iyaye a kauyukan kasar Ghana sukan zabi 'ya'yansu su yi kiwo ko noma ko kuma talla a kan hanyoyi fiye da zuwa makaranta. Juapong wani kauye ne a Tongu Arewacin Ghana, kamar yadda kowane mazaunin masu karamin karfi yake fama da rashin abubuwan more rayuwa irin su rashin hanyoyi da tsafta da kuma rashin makarantu haka abin yake a garin na Juapong. A iya cewa mafita daga cikin irin wadannan matsaloli ita ce ilimi kamar yadda Princess Abiwu mai makarantar 'Redeemed Royal International School' ta ce ba ta gajiyawa wajen jan hankalin Iyaye da su saka 'ya'yansu a makaranta
" A kullum in ba na cikin makaranta to na je ziyarar iyayen yara ne inda nake tatttaunawa da su don gano matsalolinsu, tare da jan hankalinsu kan su tura 'ya'yansu makaranta".
Ita dai Princess wacce ta ajiye aikinta don wannan makaranta da ta kirkira wacce ake karatu kyauta, lokuta da dama takan hadu da yaran da suke wa iyayensu wasu ayyuka ba sa zuwa makaranta.
Wannan gudummawa ta Princess Abiwu ta sa iyaye da dama gamsuwa da darajar da Ilimi ke da ita. Mabel wata kaka ce wacce ta ce babu shakka akwai ribar da za a tsinta a ilimi.
" In ka dubi yadda yara suke karatu a gida saboda koyar da su da aka yi a makaranta, mu iyaye mukan cika da farin ciki saboda mun tabbatar za a samu wani abu mai kyau daga karshe"
An dai fara wannan makaranta ne da dalibai bakwai amma a halin yanzu akwai dalibai 150 masu daukan darasi, duk da cewar ta kirkiri wannan makaranta ce da kudinta. Sai dai in aka yi la'akari da yadda ake dada samun karuwar dalibai a makaranatar, a iya cewa ya zama tilas Princess Abiwu ta bukaci taimako don kudin makaranta ta kafafen sada zumunta na zamani.