1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kashedi ga shugaban ƙasar Siriya

August 11, 2011

Ƙwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin ɗaukar mataki akan ƙasar Siriya da ke ci-gaba da yin amfani da ƙarfin soji wajen murƙushe zanga zangar ƙin jinin gwamnati

https://p.dw.com/p/12EsH
Shugaba Bashar Al-AssadHoto: AP

ƙwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya gargaɗi shugaba Bashar Al Assad na Siriya da ya dakatar da yin amfani da ƙarfin soji wajan murƙushe masu yin zanga zangar ƙin jinin gwamnatin. Manbobin ƙwamitin waɗanda suka tabka zazzafar muhawara a jiya a asirce, wadda akan ta aka samu rarrabuwar kawunan tsakanin ƙasashen, wajan ɗaukar mataki akan shugabannin ƙasar na Siriya sun ce tilas ne a ƙara matsa ƙaimi.

Ƙasashen Rasha da China suna buƙatar da a bi hanyoyin diplomasiya domin warwware matsalar yayin da Amirka da ƙasashen Turai ke son a ɗauki matakin ladabtarwa. A wata ganawa da shugaba Assad ɗin ya yi da jakadun ƙasashen da ke cikin ƙwamitin sulhun a karon farko ya amince cewar sojojinsa sun aikata kura-kurai. Ƙungiyoyin kare hakin bil adama sun ce mutane kusan dubu biyu suka mutu a sakamakon yamutsin da aka soma tun a cikin tsakiyar watan Maris da ya gabata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar