1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci ɗaukar mataki a kan Siriya

December 2, 2011

Yayin da hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar mataki a kan Siriya, a waje guda Rasha da ƙasar Sin sun soki lamirin matakin.

https://p.dw.com/p/13LoA
Navi Pillay shugabar hukumar kare haƙƙin bil Adatama ta Majalisar Ɗinkin DuniyaHoto: AP

Shugabar hukumar kare haƙƙin bil Adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya Navi Pillay ta yi kira ga manyan ƙasashen duniya su ɗauki mataki domin kare jama'a fararen hula a Syria daga uƙubar da gwamnatin Syrian ke gana musu. Sai dai kuma kiran ya ci karo da kakkausar martani daga ƙasashen China da Rasha. Shugabar hukumar kare haƙƙin bil Adaman ta ce mutane fiye da 4,000 ne suka rasa rayukansu a dirar mikiyar da sojoji suka yi a kan masu zanga zanga tun bayan ɓarkewar rikicin a watan Maris yayin da wasu mutanen 14,000 kuma ake kyautata tsammanin an tsare su a gidajen yari. " Ta ce a ra'ayi na bisa binciken da muka gudanar kan al'amuran dake faruwa, akwai buƙatar hukunta waɗanda suka aikata wannan ta'asa daga ƙololuwa bisa laifukan cin zarafin bil Adama".

Hukumar kare haƙƙin bil Adaman ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da Syria bisa cin zarafi da keta haddin bil Adama. A babban taron ta da ya gudana a birnin Geneva, daga cikin ƙasashe 46 mambobin hukumar, ƙasashe 37 suka kaɗa ƙuri'ar goyon bayan daftarin ƙudirin da ya yi Allah wadai da gwamnatin ta Syria, yayin da ƙasashe shida suka ƙaurace, kasashe huɗu kuma da suka haɗa da Rasha da kuma China suka kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Zainab Mohammed Abubakar