1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar wakilan Amurka ta amince da dokar sayarwa Indiya da makamashin nukiliya

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYi

Majalisar wakilan Amurka ta amince da wata doka ta tarihi wadda ta yarda a sayarwa Indiya makamashin nukiliya da fasaharsa don amfanin farar hula. Mafi rinjaye na ´yan majalisar sun kada kuri´ar amincewa da doka wadda yanzu ta ke gaban majalisar dattijan don a albarkace ta kafin shugaba GWB ya sanya mata hannu ta zama doka. A karkashin shirin dokar wadda ake takaddama a kai, Indiya wadda ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar da ta haramta yaduwar makaman nukiliya ba, za´a ba ta damar yin amfani da fasahar samar da makamashin nukiliya ga farar hula yayin da ita kuma zata yarda kasashe duniya su yi bincike akan tashoshinta na nakuliya. Masu adawa sun yi gargadin cewa shirin zai kawo cikas wajen daukar matakai akan bijirarrun kasashen masu mallakar makaman nukiliya kamar KTA da Iran.