1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Turkiya da amince tura sojoji Siriya

Mohammad AwalOctober 4, 2012

Majalisar dokokin Turkiya ta amince da kudirin turo sojoji tsallaken iyaka zuwa Siriya, bayan hallaka 'yan kasar biyar.

https://p.dw.com/p/16Jxc
Hoto: Bulent Kilic/AFP/GettyImages

Majalisar dokokin ƙasar Turkiya ta amince rundunar sojan ta ƙaddamar da samame tsallaken kan iyaka cikin ƙasar Siriya, sakamakon harin da aka kai wanda ya janyo hallaka mutane biyar cikin Turkiya.

Wannan amincewa da majalisar dokokin Turkiyar ta yi, ya baiwa gwamnatin ƙasar damar tura sojojin cikin ƙasar Siriya, domin daƙile duk wani yuwuwar sake harbo makami daga ƙasar ta Siriya.

Wannan ƙadiri na amfani da ƙarfi ya samu gagarumin rinjaye cikin majalisar dokokin, inda 'yan majalisu 320 su ka amince, yayin da 129 daga cikin 'yan majalisar su ka jefa kuri'ar ƙin amincewa.

Ankara Türkei Parlament Abdullah Gul Präsident
Majalisar dokokin TurkiyaHoto: dapd

Martanin na ƙasar ta Turkiya zai zama na farko daga ƙasashen ketere cikin watanni 18 na rikicin ƙasar ta Siriya. Mahukuntan Turkiya sun ce Siriya ta amince da cewa daga cikin ƙasar aka kai harin da ya hallaka fararen hulan Turkiya biyar. Turkiya ta nemi haɗin kai daga ƙungiyar tsaro ta NATO ko OTAN wadda ta ke kasancewa mamba.

Tuni shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cikekken goyon baya ga ƙasar ta Turkiya cikin wannan taƙaddama da Siriya:

Tag der Deutschen Einheit
Shugaban gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

"Muna tare da Turkiya ko wani lokaci kai da fata. Ministan harƙoƙin waje ya tuntuɓi ƙasar. Mu na da tuntuɓa tsakani, ko wani lokaci, kuma a ko wata sa'a."

Anasa ɓangaren ministan harƙoƙin wajen ƙasar ta Jamus Guido Westerwelle, ya buƙaci Siriya ta shiga haiyacinta, domin kaucewa shiga rikicin da ya fi ƙarfinta:

"Muna buƙatan gwamnatin Shugaba Assad cikin gaggawa ta tabbatar da kare ɗiyaucin ƙasar Turkiya, tare da mutunta sauran makwabta. Na bayyana ƙarara cewa ƙungiyar tsaron NATO ta bayan Turkiya a matsayin ta na mamba. Wannan abu ne da bubu shakka, amma muna kira da a shiga tattaunawa kan wannan sabon tashin hankali."

Tunda fari mataimakin Fira ministan ƙasar ta Turkiya, Bulent Arinc, ya buƙaci ƙungiyar tsaro ta NATO ko OTAN ta duba halin da ake ciki:

"Wannan farmaƙi kan ƙasar Turkiya kuma ya hallaka fararen hula. Ya rage wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki mataki kan wannan lamari, bisa 'yancin da ƙasa ke da shi. Kuma Turkiya ta na cikin ƙungiyar NATO. Bisa tsarin NATO, duk wanda ya tabo ɗaya daga ciki, tamkar ya taɓo dukkanin sauran ƙasashen game da sakamakon da zai biyo baya."

Ƙasar Rasha mai alaƙa da gwamnatin Siriya, ta bayyana samun tabbataci cewa mahukuntan Damuscus sun tabbatar da cewa wannan harin roka tsautsayi ne, kuma za a kare sake faruwar lamarin, inda ministan yaɗa labaran ƙasar ta Siriya ya miƙa saƙon ta'aziya ga Turkiya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai yi taro, bisa buƙatar ƙasar Turkiya, wadda ta nemi taka wa Siriya burki, tare da ɗaukan duk matakan da su ka dace.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani