1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badawi ya samu lambar yabo ta Sakhrov ta Tarayyar Turai

Yusuf BalaOctober 29, 2015

Shi dai Raif Badawi an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan kaso tare da bulala dubu daya saboda kalaman batanci ga addinin Islama.

https://p.dw.com/p/1GwWq
Startbild Video Raif Badawi

Uwargidan dan fafutikar kare hakkin bil Adaman nan na kasar Saudiyya wato Raif Badawi ta bayyana a ranar Alhamis din nan cewa samun dama ga mijinta na lashe lambar yabo ta majalisar kungiyar Tarayyar Turai Sakharov kan kare hakkin bil'Adama wata alama ce ta kara samun karfin gwiwa da fata ga mai gidan nata.

Ta mika godiyarta ga majalisar ta kungiyar Tarayyar Turai inda ta ce ta yi farinciki sosai kan wannan lambar yabo kamar yadda ta fada wa kamfanin dillancin labaran AFP amadadin mai gidan nata.

Shi dai Raif Badawi an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan kaso tare da bulala dubu daya saboda ya yi kalaman batanci ga addinin Islama.