1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Iran ta amince da yarjejeniyar nukiliya

Gazali Abdou tasawaOctober 13, 2015

Da kuri'u 161 daga cikin 233 majalisar dokokin kasar ta Iran ta amince da yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta cimma da kasashen duniya a cikin watan yulin da ya gabata.

https://p.dw.com/p/1GnMK
Iran Expertenrat
Hoto: picture-alliance/AA

Majalisar dokokin kasar Iran ta kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta cimma da kasashen duniya ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata bayan wata zazzafar mahawara tsakanin masu goyan baya da kuma masu adawa da ita a majalisar.

Da kuri'u 161 daga cikin 233 ne dai majalisar dokokin kasar ta Iran ta amince da dokar wacce ta kunshi ayoyi tara daga ciki har da wacce ta tanadi cewa babu wata gwamnatin kasar ta Iran da a nan gaba ke da izinin kera ko kuma yin amfani da makamin nukiliya.

Sai dai kuma ayar dokar da ta amince da yarjejeniyar nukiliyar ta kuma tanadi cewa yarjejeniyar ta tanadi mutunta juna da yin aiki kafada da kafa kuma hukumomin tsaron kasar ta Iran na da hurumin yi wa dokar gyaran huska a duk lokacin da kasar ta Iran za ta fuskanci wata bazrazana ga rayuwa ko zaman lafiyarta.