1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran adawa a Rasha ya samu lambar yabo

Zainab Mohammed Abubakar
October 20, 2021

Jagoran adawa da gwamnatin Rasha Alexei Navalny, ya samu lambar yabo ta Sakharov daga majalisar dokokin Turai kan kare hakkin dan Adam na shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/41vEz
Russland Moskau Oppositionsführer Alexej Nawalny 2019
Hoto: Sefa Karacan/AA/picture alliance

Mai shekaru 45 da haihuwa kuma mutumin da ya tsallake rijiya da baya, bayan saka masa guba a watan Augustan 2020 Navalny, yana zaman gidan yari na shekareuu biyu da rabi.

Kasashen EU dai sun kakaba wa Rasha takunkumi dangane da sanya wa jagoran adawar guba da kuma tsare shi da ta yi. Kungiyar 'yan majalisa mafi girma ta tarayyar Turai da ake kira EPP Group ce ta sanar da bashi lambar yabon a shafinta na Twitter, saboda fafutukarsa wajen kalubalantar shugaban Rasha Vladimir Putin.