1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tanzaniya ta amince da sauye-sauyen zabe

Suleiman Babayo LMJ
February 2, 2024

'Yan majalisar dokokin kasar Tanzaniya sun kada kuri'ar amince da sauye-sauye ga dokokin zaben kasar abin da 'yan adawa suke gani har yanzu da saura bisa sauyin fasalin da ake bukata.

https://p.dw.com/p/4bzKW
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta Tanzaniya
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta TanzaniyaHoto: Presidential Press Service Tanzania

'Yan majalisar dokokin kasar Tanzaniya a wannan Jumma'a sun amince da sauye-sauye ga dokokin zaben kasar, inda tuni babbar jam'iyyar adawa ta Chadema ta yi watsi da matakin saboda rashin cika muradun da 'yan adawa suka gabatar tun shekara ta 2020 lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Marigayi John Magufuli.

Karin Bayani: Madugun 'yan adawa na Tanzaniya ya koma gida

Amma Shugaba Samia Suluhu Hassan wadda ta dauki madafin iko a shekara ta 2021, bayan mutuwar Marigayi John Magufuli, ta tsaya kai da fata cewasauye-sauye za su inganta tsarin dimukaradiyya a kasar da ke yankin gabashin Afirka. 'Yan adawa suna korafi ganin cewa shugabar kasar za ta nada biyar daga cikin mambobi 10 na hukumar zabe, yayin da ake shirin zaben shekara mai zuwa ta 2025.