Majalisar dokokin Masar za ta zauna a wannan Talata
July 9, 2012Da ya ke wa manema labarai jawabi, kakakin majalisar ya ce za su zauna a goben da misalin karfe goma agogon GMT.
Majalisar dai ta ɗauki wannan matsayi ne bayan da sabon shugaban ƙasar Muhammad Mursi a jiya lahadi ya bada umarnin ta koma zaman ta, sai dai kuma sojojin ƙasar da ma dai kotun ƙolin kasar ba su amince da wannan matsayi da shugaban ƙasar ya ɗauka ba inda kotun ta ce za ta zauna a gobe (Talata) domin duba wannan mastayi da shugaban ƙasar ya ɗauka don sanin tudun dafawa.
Masu sanya idanu kan siyasar kasar ta Masar dai na ganin wannan lamari ka iya jefa jaririyar gwamnatin Mursi cikin rikici da rundunar sojan ƙasar da ma dai ɓangaren shari'a.
Tuni dai wasu jam'iyyu ciki har da jam'iyyar Egyptian Social Democratic Party wadda ke da wakilai a majalisar su ka fara yin tur da wannan matsayi na shugaba Mursi da kakakin majalisar dokokin ƙasar inda su ka ce hakan karen tsaye ne ga ɓangaren shari'a to sai dai jam'iyyar 'yanuwa Musulmi ta Shugaba Mursi ta ce sam ba karen tsaye ta dau aniyar yi ga ɓanaren na shari'a ba.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi