1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin Japan ta amince da Yasuo Fukuda a matsayin saban Praminista

September 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuAJ

Majalisar Dokokin ƙasar Japan ta kaɗa kuri´ ar amincewa da Yasuo Fukuda, a matsayin saban Praminista, wanda zai gaji Shinzo Abbe da yayi murabus daga muƙamin sa.

Yasuo Fukuda, mai shekaru 71 a dunia, ya samu ƙuri´u 338 na yan majalisar dokoki.

Sannan nan gaba a yau, majalisar wakilai zata kaɗa ƙuri´a, don amincewa ko kuma yin watsi da Fukuda.

Saidai babu tabbas ya samu karɓuwa a wannan majalisa, ta la´akari da cewar, jam´iyar adawa ke da rinjaye a cikin ta.

Masu kulla da harakokin siyasa a ƙasar Japan, na hasashen cewar, yin watsi da Yasuo Fukuda, zai ƙara tsunduma ƙasar a cikin wani saban rikicin siyasa.

To amma ko da wannan majalisa ta bayana adawa da Fukuda dokokin ƙasa sun bashi damar jagorantar gwamnati.

A nasa ɓangare, tsofan Praminista Shinzo Abbe, ya nemi gafara ga jama´a, a game da shawara da ya ke wa kansa cikin garaje ta yin murabus.