1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Girka ta amince da shirin tsuke aljihun gwamnatin

November 8, 2012

Shirin zai bai wa ƙasar samun ƙarin tallafi na kuɗaɗe daga ƙungiyar Tarrayar Turai da asusun ba da lamuni na duniya IMF,domin yaƙi da matsalar tattalin arziki da ƙasar ta ke fuskanta

https://p.dw.com/p/16fZO
Greece's Prime Minister Antonis Samaras addresses parliamentarians during a session in Athens November 7, 2012. Greek police fired teargas and water cannons to disperse thousands of protesters who flooded into the main square before parliament on Wednesday in a massive show of anger against lawmakers due to narrowly pass an austerity package.The violence erupted as a handful of protesters tried to break through a barricade to enter parliament, where Samaras is expected to barely eke out a win for the belt-tightening law despite opposition from a coalition partner. REUTERS/Yorgos Karahalis (GREECE - Tags: POLITICS BUSINESS)
Hoto: Reuters

Majalisar dokokin ƙasar Girka ta amince da shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin, a yayin da a yau aka shiga  cikin kwanaki na biyu na zanga zangar da duban jama'ar ƙasar suke yi domin yin addawa da shirin.

Tsarin na gwamnatin  na rage kuɗaɗen da gwamnatin ta ke kashe wa  da biliyan 13 da rabi ,wanda ke buƙatar samu ta barakin majalisar gabannin samun tallafi na ƙungiyar Tarrayar Turai da asusu bada lamuni na duniya  kimanin biliyan 31;ya samu amincewa a majalisar da ƙaramin rinjayen da ya zarta ƙuri'u 151.

Fra ministan  girka Antomi Samaras ya sanar da cewar wannan abi ne da ya zama ruwan dare gama dunia ya ce dole sai an daure.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita      : Mahamadou Awal Balarabe