1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya zata tura wakilai zuwa Sudan

May 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuxW
A cikin mako mai zuwa MDD zata tura manyan wakilanta guda biyu yankin Darfur dake fama da rikici a yammacin Sudan, inda zasu gudanar da shawarwari game da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar yankin cikin gaggawa. Tsohon wakilin MDD na musamman Lakhdar Brahimi zai shugabanci shawarwari da za´a yi da gwamnatin Sudan, inda za´a tattauna game da rawar da MDD zata taka wajen aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar da kuma yadda zata karbi ragamar rundunar kiyaye zaman lafiya wadda kungiyar tarayyar Afirka ta girke a lardin Darfur. Shi dai Lakhdar Brahimi dan kasar Aljeriya yana da kyakkyawar dangantaka da kasashen Afirka da na Larabawa, a saboda haka zai iya taka muhimmiyar rawa a kokarin da MDD ke yi na kawo karshen rikicin lardi na Darfur.