Majalisar Dinkin Duniya za ta tura runduna zuwa Mali
April 26, 2013Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) zai yi haka ne kafin tura dakarun Afirka zuwa wannan kasa da za a yi daga watan Yuli. Rundunar soji da 'yan sandan da MDD ta ya yi wa suna "Minusma" za ta taimaka wa gwamnatin Mali a yakin da ta ke yi da 'yan kishin islama da 'yan aware da ke arewacin kasar domin maido da kwanciyar hankali.
A dai halin yanzu sojoji Faransa 4000 ne ke taimaka wa dakarun kasar ta Mali da na kasashe makwabta da ke yaki da 'yan tawayen. Tun wasu watannin kenan da Faransa da kasashen Afirka ke yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta karbi wannan aiki, ta kuma samar da kudin tallafa wa dakarun Afirka da za a tura zuwa kasar ta Mali.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar