1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Tallafi ga tattalin arziki saboda Corona

Mohammad Nasiru Awal MAB
March 26, 2020

Za a yi amfani da kudaden wajen fadada inshorar marasa aikin yi da bangaren kiwon lafiya musamman a jihohin da cutar Coronavirus ta fi shafa.

https://p.dw.com/p/3a2vx
Washington: Das Kapitol - Sitz des US-Kongresses
Hoto: picture-alliance/J. Schwenkenbecher

Da gagarumin rinjaye majalisar dattawan Amirka ta amince da wani gagarumin tallafi ga tattalin arzikin kasar da ya kai Dala tiriliyan biyu don tinkarar nakasun da annobar Corona za ta yi wa tattalin arzikin kasar.

A cikin wannan makon ake sa ran majalisar wakilai a nata bangare za ta amince da shirin tallafin da za a yi amfani da shi wajen fadada inshorar marasa aikin yi. Hakazalika bangaren kiwon lafiya musamman jihohin da cutar Coronavirus ta fi shafa, za su samu karin tallafi na biliyoyin dala. Kanana da matsakaitan kamfanoni za su amfana da tallafin.

A kuma can kasar Italiya yaduwar Coronavirus ta dan yi baya kwanaki hudu a jere, inda yawan masu harbuwa da cutar ya karu da kashi 7.5 cikin 100, adadin da ke zama mafi karanci tun bayan bullar annobar a cewar hukumomin kiwon lafiya. A jimilce yawan wadanda suka mutu a cikin sa'o'i 24 ya kai mutum 683, abin da ya sa yawan wadanda suka mutu sakamakon COVID-19 ya zuwa ranar Laraba a kasar ta Italiya ya kai 7503. Kusan dubu 74 da 400 suka kamu da ita.