1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Bundestag tayi zaman farko bayan zabe

October 22, 2013

Sabuwar majalisar Bundestag tayi zaman taron farko bayan zabe amma jam'iyun adawa ba za su iya kalubalantar aiyukan gwamnati ba.

https://p.dw.com/p/1A45D
Hoto: AFP/Getty Images

Ranar Talata a Berlin, sabuwar majalisar dokokin Jamus da aka zaba kwanaki 30 da suka wuce tayi zaman taronta na farko, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. To sai dai a yayin da manyan jam'iyu biyu a majalisar wato CDU da CSU da kuma SPD suke shirin shiga shawarwarin kafa gwamnatin hadin gwiwa, yan kananan jam'iyu biyu da suka rage a majalisar, wato jam'iyar Linke ta masu neman canji da kuma jam'iyar Greens wakilansu a majalisar basu taka kara sun karya ba. Yayin da manyan kam'iyun biyu suke da wakilai 504 gaba daya, su kuwa jam'iyun na adawa wakilansu basu wuce 127 ba. Hakan ya sanya a rika kwatanta jam'iyun na adawa kamar dai yan tsaki ne a gaban kura a majalisar ta Bundestag.

Kafin zaben majalisar dokokin da aka yi ranar 22 ga watan jiya, yan adawa suna da ninki biyu ne na yawan wakilan da suka samu bayan zaben, saboda kasancewar jam'iyar SPD a matsayin mai adawa. Idan har SPD ta yanke shawarar shiga gwamnati, hakan zai jefa jam'iyun adawa da suka rage cikin wani hali mai wahala a game da neman gyara ko sukan aiyukan gwamnatin tarayya. Kamar yadda aka saba, yan adawa suna da hanyoyi masu yawa na yin haka. Suna iya neman gwamnatin tilas ta amsa tambayoyi a game da aiyukanta, suna kuma iya tilastawa a kafa kwamitocin bincike kan wani abin da suke ganin gwamnati tayi ba daidai ba, suna kuma iya neman kotun kare tsarin mulki ta duba wasu dokoki na gwamnati, idan suna da ra'ayin sun sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Masanin al'amuran siyasa Stephan Bröchler yace:

A halin da majalisar dokokin ta Jamus tace ciki yanzu, duka wadannan abubuwa ne da ba zasu yiwu ba. Yan jam'iyar Greens da masu ra'ayin neman canji basu da damar kiran kafa wani kwamitin bincike, ba kuma zasu iya neman majalisar Bundestag ta kada kuri'ar neman amincewa ko kin amincewa da gwamnatin dake mulki ba, ba kuma zasu iya neman kotun kare tsarin mulkin tarayya ta duba wata doka da majalisar ta gabatar ba, ba zasu kuma iya kai kara gaban kotun Turai ba. A hakika, duka wadannan matsaloli ne da tilas a warware su tukuna.

To sai dai Jan van Aken, dan majalisar ta Bundestag daga jam'iyar Linke ta masu neman canji yace jam'iyarsa ba zata ji nauyin gabatarwa majalisar tambayoyi a duk lokacin da take ganin hakan ya dace ba. Ko da shike gwamnati zata rika kokarin boye wasu aiyukan ta ko kura-kuranta, amma jam'iyarsa ba sabuwa bace wajen matsawa gwamnati tayi bayanin aikace-aikacen nata.

Bundestag konstituierende Sitzung Plenarsaal 22.10.2013 Merkel
Shugaban gwamnati Angela Merkel(tsakiya) a majalisar BundestagHoto: Odd Andersen/AFP/Getty Images

Yace babu shakka gwamnati ta kware wajen kin amsa tambayoyin da suka shafi aiyukanta, to amma mu din ma mun kware wajen gabatar da tambayoyin da suka dace. Ina ma iya nuni da halin da muke ciki yanzu da abubuwan da muka gano a game da batun sayarwa Syria sinadarin kera makamai masu guba ko kuma cinikin makaman Jamus a ketare a yan shekarun nan. Hakan ya nuna mana cewar gwamnatin ba zata iya yin watsi da tambayoyi ba komai kankantarsu.

A bisa ra'ayin Hans Josef Fell, wanda tun daga shekara ta 1989 yake wakiltar jam'iyar Greens a majalisar dokokin taraiya, akwai hanyoyi da dama na nuna angizo a aiyukan da wakilan gwamnati suke tafiyarwa. Ana iya magana da juna a kwamitoci na kwararru, inda wakilan gwamnati da na yan adawa suke tattaunawa da juna kan al'amura masu muhimanci da suka shafi kasa baki daya.

Kananan jam'iyun na adawa a majalisar dokoki ana kuma sa ran zasu sami goyon baya da taimako daga wani bangaren dabam. Uwe Jun, masanin al'amuran siyasa a jami'ar Trier, yace ya kan lura da karin adawa a wajen majalisar taraiya a duk lokacin da aka kafa gwamnatin hadin gwiwar manyan jam'iyu. Jun ya ambaci kungiyoyin m a'aikata kungiyoyin kare bukatun al'umma da kafofin yada labarai.

Bundestag konstituierende Sitzung Plenarsaal 22.10.2013
Wakilai cikin majalisar dokokin Jamus a zaman farko bayan zabeHoto: Reuters

Yace hakan zai yi jagora ga samun wani salo na adawa da gwamnati wanda ba a majalisar dokoki yake ba. Kafofin yada labarai zasu taka muhimiyar rawa, haka nan kungiyoyi na adawa da za'a kafa a wajen majalisar dokokin suma zasu taka muhimmiyar rawa.

To sai dai Dieter Dehm na jam'iyar masu neman canji yace kafofin yada labarai babu wata muhimmiyar rawa da zasu iya takawa saboda tsakanin shekaru 30 da suka wuce zuwa yanzu, kafofin yada labaran sun zama yan amshin shata, wato a takaice sun daina zama masu sukan gwamnati a duk inda tayi wani abin da ba daidai ba.

Mawallaafi:Wolfgang Dick/Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh