1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Amirka ta taso da batun kisan Khashoggi

Mahmud Yaya Azare MA
December 14, 2018

Ga dukkan alamu, masu hannu a siyasar Amirka sun tasan ma tilasta kasar daukar matsaya ta hukunci kan Yerima mai jiran gado na Saudiyya dangane da zargin kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

https://p.dw.com/p/3A7TZ
Bildkombo Saudi-Arabien | Jamal Khashoggi & Mohammed bin Salman

'Yan majalisar dattawa a Amurka, sun amince da gagarimin rinjaye da wani kudirin da ke zargin yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammad Bin Salman, da kisan dan jaridan nan mai sukar masarautar Saudiyyar, Jamal Khashoggi, lamarin da ke ci gaba da jawo cece-kuce a tsakanin masharhanta.

Kakakin majalisar dattawan Amirka, Boob Cocker, ya dora alhakin kisan dan jaridar kan Bin Salman, batun da ya ce ‘yan majalisar sun amince kansa da gagarumin rinjaye, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an aiwatar da shi.

Wakazalika, majalisar dattawan ta sake amincewa da wani kudurin da ke dora wa Saudiyyar alhakin kisan kare dangin da ake yi wa fararen hula da yara kanana a kasar Yemen, ta bakin Barnard Sanders.

Tuni dai masu fashin baki a kasar Saudiyya, irin su Dr. Sulaiman Al-Uqaili suka siffanta kudurorin da wani shakulatun bangaron da ba zai tayar wa da mahukunatan da al’ummar Saudiyya da hankali ba.

To sai dai kamar yadda Dr. Jamal Antali, wani mai fashin baki kan alakar Amirka da Saudiyya ke gani babu ta yadda za a yi a ce wadannan kudurorin ba za su shafi fadar mulkin Riyadh ba