1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta gargaɗi Isra'ila da Siriya

May 6, 2013

Babban sakataran MDD Ban Ki Moon ya ce ya damu so sai dangane da halin da ake ciki bayan hare haren da Isra'ila ta kai a Siriya.

https://p.dw.com/p/18SiU
U.N. Secretary General Ban Ki-moon addresses participants during the signing ceremony of the Peace, Security and Cooperation Framework for the Democratic Republic of Congo and the Great Lakes, at the African Union headquarters in Ethiopia's capital Addis Ababa Feburary 24, 2013. A U.N .-mediated peace deal aimed at ending two decades of conflict in the east of the Democratic Republic of Congo was signed on Sunday by leaders of Africa's Great Lakes region in the Ethiopian capital Addis Ababa. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Unterzeichnung Friedensabkommen im KongoHoto: Reuters

Ban Ki Moon ya ce; ci gaba da yin tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu,na iya zama wata babbar fitina a yankin baki ɗaya wanda yaƙi ya ɗaiɗaita.

A cikin wata sanarwa da ya bayyana babban magatagarda na MDD ya yi kira ga sasan biyu da su yi sassauci tare da kawo ƙarshen kai ruwa rana da ake yi tsakanin kasashen biyu. Hare haren waɗanda su ne na biyu a cikin sao'i 48 da Isra'ila ta kai a Siriya, sun hadasa lallacewar wata cibyar binciken kimiyyar ta ƙasar wacce kasashen duniya ke fargaban cewa cibiyar sarafa makamai ce, masu guba. Isra'ila dai ta ce, ta kai harin ne domin hanna isar da wasu makamai masu linzami da gwamnatin Siriyan ta shirya bai wa mayanan Kungiyar Hezbollah a Libanon da ke makoftaka da Siriyar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Editan : Yahouza Sadissou Madobi.