Zinédine Zidane zai fice daga Real de Madrid
May 31, 2018Talla
Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da Real Madrid ta samu nasara ta uku a jere ta lashe kofin zakaru na Turai.
A wani taron manema labarai da ya yi Zidane dan shekaru 45 da haifuwa wanda ya zo Real Madrid a shekara ta 2016, ya ce ba zai ci gaba da horar da 'yan wasan ba na Real Madrid a shekarr badi.
Ya zuwa yanzu dai Zizou kamar yadda ake yi masa la'akabi bai ce ba zai sake neman wani klub din ba don ci gaba da yin aikinsa na horaswa.