1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar 11 sun mutu sabon hari

Abdul-raheem Hassan
November 6, 2021

Wani sabon harin 'yan bindiga ya sake halaka dakarun gwamnatin Nijar 11, mutum daya ya jikkata wasu 9 sun bace bayan bude musu wuta a wani sansanin sojoji a Dagne da ke yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/42ezw
Niger Armee | Attentat auf ACTED Hilfsorganisation
Hoto: AFP/B. Hama

Wata sanarwar daga ma'aikatar harkokin tsaron Nijar na zaton mayakan jihadi da suka saba kai farmaki kan iyakar Burkina Faso da Mali ne suka kaddamar da hari kan sojojin kasar da manyan makamai yayin da suka zo kan babura da motoci.

Harin ya faru ne kwanaki kalilan bayan wani mummunar harin kwantan bauna da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 69, matakin da ya sa gwamnatin Nijar ayyana makoki na kwanaki biyu.