1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari mafi muni a Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
June 5, 2021

Majiyoyin tsaro a Burkina Faso sun ba da rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai sun afka wa garin Solhan da ke a yankin kudancin kasar inda suka kashe mutane sama da guda  dari.

https://p.dw.com/p/3uThD
Burkina Faso Soldaten
Hoto: Olympia de Maismont/AFP/Getty Images

Mutane wadanda suka kai harin a daran Juma'a wayewar Asabar sun kone kasuwar garin kurmus tare da kashe mata da yara da mazaje wanda ake tsamanin adadin zai iya zarta dari. Wannan dai shi ne hari mafi muni da 'yan ta'addar suka kai a Burkina Faso tun bayan harin da ya afku a shekara ta 2015. A halin da ake ciki gwamnatin ta ce ta tura sojoji domin bin sawun  wadanda suka aikaita ta'asar.