1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahamadou Issoufou na ban kwana da mulki

Gazali Abdou Tasawa AH
April 1, 2021

A Jamhuriyar Nijar ranar karshe ta wa’adin mulkin shekaru 10 da Shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya yi a kan karagar mulkin kasar inda zai mika sandar mulki ga sabon zababben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3rVey
Niger Symbolbild Fahne | Mahamadou Issoufou
Hoto: Boureima Hama/AFP

Shugaban Mahamadou Issoufou ya karbi karagar mulkin Nijar a karon farko a shekara ta 2011, kana ya samu karin wa’adin shekaru biyar a zaben shekara ta 2016. A tsawon shekaru 10 da ya yi yana mulki ya ga yabo daga wasu ‘yan kasa ya kuma fuskanci suka daga wasu dangane da yadda ya tafiyar da mulkinsa da kuma ayyukan da ya yi ko ya kasa yi a cikin kasa. A jajibirin mika mulkinsa ko wani darasi za a iya cewa an samu a tsawon shekaru 10 na mulkinsa. To sai dai a daidai loakcin da adawa ke cewa ba ta ga wani abin alkhairin da Nijar ta samu a tsawon shekaru 10 na mulkin Shugaba Issoufou ba, Malam Assoumana mahamadou kakakin jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki na ganin ayyukan da shugaban ya yi wa kasar ba a boye suke ba da har duniya ta shaida ta hanyar ba Shi lambobin yabo na iya shugabanci.

Suka da yabo da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ke sha a karshen mulkinsa

Niger Wahlkampf Mahamadou Issoufou Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Mohamed Bazoum

Bayan 'yan siyasa har a tsakanin  sauran ‘yan kasa ma ana samun irin wannan sabanin ra’ayi kan sakamakon mulkin shekaru 10 na shugaba Issoufou yayin da wasu suke yaba ayyukan da ya yi wasu na yin mummunar kushewa.