Mahajjata sun isa Muzdalifah bayan Arfa
July 30, 2020Wannan zuwa Muzdalifah na zuwa ne bayan da mahajjata suka shafe yini guda na hawan Arfa da ke zama muhimmin ginshiki na aikin Hajji. Sai dai addu'o'in maniyatan sun gudana ne cikin tsauraran matakan tazara tsakaninsu tare da sanya takunkumi don kauce wa kamuwa da cutar corona. A kasar ta Saudiya dai mutane akalla dubu 272,590 ne suka kamu da covid-19, ciki har da mutum 2,816 da cutar ta yi sanadiyyar mutuwarsu
A bana dai kasar Saudiyya ta haramta wa baki shigowa kasar don sauke farali sakamakon bullar cutar numfashi ta corona. Mutane dubu 10 da ke da zama a kasar mai tsarki ne kawai suka samu damar gudanar da bautar. Shi dai aikin hajji, yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci da ake so kowanne Musulmi ya yi, ko da sau daya ne a rayuwa, idan dai yana da hali da kuma koshin lafiya.