1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta fadi sirrin maganin Corona

April 9, 2020

Wasu likitocin China da ke aiki a asbitin masu Coronavirus a birnin Wuhan sun ce maganin cutar HIV/AIDS na yin aiki wurin rage kaifin cutar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3ai1s
China Wuhan provisorisches Krankenhaus für Coronavirus-Patienten
Hoto: picture-alliance/AP/Chinatopix

Likitocin sun ce tun a watan Janairun da ya gabata suke amfani da maganin mai suna Kaletra. Jagoran likitocin mai suna Zhang Dingyu ya ce a cikin kwana biyu zuwa uku da suka fara bayar da maganin HIV din ga masu Corona, sun ga hunhunsu ya sauya kuma sun fara samun sauki.

Sai dai a watan da ya gabata wani bincike ya ce maganin HIV ba ya iya aiki a kan cutar Corona, to amma jagoran likitocin na Wuhan ya hakikance cewa  su sun jarraba maganin HIV kuma ya musu aiki.