1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita ga rikicin gina dam a kogin Nilu

June 18, 2013

Masar da Ethiopia suka ce tattaunawa ce hanyar da ta fi dace wa ga warware takaddama a kan gina dam a kogin Nilu.

https://p.dw.com/p/18rjI
Damm-Krise zwischen Äthiopien und Ägypten. Copyright: Nael Eltoukhy, 5 Juni 2013, Ägypten
Hoto: Nael Eltoukhy

A wannan Talatar (18.06.2013)ce gwamnatocin kasashen Masar da Ethiopia suka bayyana cewar rungumar tattaunawa ce mafi dace wa wajen shawo kan cece-kucen da ke tsakaninsu game da anniyar da kasar Ethiopia ta bayyana na gina babban dam a kan kogin Nilu, wanda kuma kasar ta Masar ta dogara da ita wajen samun kusan daukacin ruwan da kasar ke anfani da shi.

A dai makonnin da suka gabata, kasar ta Masar, wadda ke zama kasa ta uku mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka ta yi ta tada jijiyar wuya game da kudirin da Ethiopia ta nuna na samar da madatsar ruwan da nufin warware matsalar wutar lantarkin da take fama da ita, wanda kuma Masar ke fargabar matakin zai rage yawan ruwan da ke da muhimmanci ga rayuwar al'ummar kasar miliyan 84.

A ranar 10 ga watan Yunin nan kuma shugaban Masar Muhammad Mursi ya bayyana cewar, ba ya kaunar shiga cikin yaki, kuma akwai zabi daban-daban da za a bi wajen warware takaddamar, wadda kuma ya sa ita Etthiopia bayyana cewar tana shirye ta kare matakin da take son dauka na gina dam din a kusa da iyakarta da kasar Sudan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu