1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madugun adawa a Senegal ya kira zanga-zanga

July 3, 2023

Madugun adawar Senegal Ousmane Sonko, ya yi kiran da a fito domin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4TL7o
Masu zanga-zanga a kasar Senegal
Hoto: Muhamadou Bittaye/AFP

Ousmane Sonko ya yi wannan kiran ne, a kokarin ganin an murkushe take-taken Shugaba Macky Sall na tsayawa takara a karo na uku.

Da yammacin yau din nan ne dai ake sa ran Shugaba Macky Sall, zai bayyana aniyarsa ta sake tsayawar a wani jawabin da zai yi.

Shugaban da aka zabe a 2012, sannan aka sake zaben sa a 2019, ya fada a 2016 cewa kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar yin takara a 2024.

Wa'adi biyu ne dai tsarin dimukuradiyyar Senegal ya amince wa shugaban kasa.

Madugun adawa Ousmane Sonko dai ya kekashe kasa, yana mai cewa lallai ne 'yan Senegal su tsaya wajen ganin Shugaba Sall bai mulke su har sau uku ba.