1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Macron na shan suka kan ziyartar Saudiyya

December 3, 2021

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sake nanata cewa bai manta da kisan da aka yi wa dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi ba.

https://p.dw.com/p/43og7
Frankreich Paris | TV Ansprache Emmanuel Macron
Hoto: CHRISTOPHE ARCHAMBAULT/AFP/Getty Images

Macron din na wannan magana ce a yayin da ya fara shan suka kan ziyarar da yake son kai wa Saudiyya a ranar Asabar. Shugaban na Faransa ya shaida wa 'yan jarida haka a dazu da rana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.


''Babu wanda nake son karewa, amma mu fada wa junanmu gaskiya, wane irin taimako za mu iya yi wa kasar Lebanon da Iraqi idan har muka yanke alaka da Saudiyya?'' inji Macron


Ganawar da shugaban na Faransa zai yi da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman za ta zama ta farko da wani shugaba daga kasashen yamma zai yi da yariman tun bayan da aka kashe Jamal Khashoggi a ofishin jakandancin Saudiyya da ke birnin Santanbul na Turkiyya a shekara ta 2018. To amma Macron ya ce hakan na da tasiri a ziyarar da yake yi a kasashen yankin Gulf.