1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta yi nadama kan rikicin Ruwanda

Abdul-raheem Hassan
May 27, 2021

Shugaba Emmanuel Macron ya ce kamalan hakuri sun yi kadan, idan aka duba rawar da Faransa ta taka a kisan kiyashin da aka yi a Ruwanda a shekarar 1994.

https://p.dw.com/p/3u3lU
Kigali | Macron Besuch in Ruanda
Hoto: AFP

Yayin wata ziyara a Kigali babban birnin kasar Ruwanda, Shugaba Macron ya ce Faransa ta dauki nauyin abin da ya faru tare da neman yafiya. Sai dai shugaban Faransa bai nemi gafara a hukumance ba, ya yi kalaman ne a wurin da aka binne mutane 250,000 da aka yi wa kisan kiyashi a birnin Kigali.

A watan Yulin shekarar 1994 ne Shugaban Ruwanda Paul Kagame ya jagoranci wata rundunar da ta kawo karshen kisan kiyashin a watan Yunin 1994, bayan da mayakan kabilar Hutu suka kashe 'yan kabilar Tutsi 800,000 cikin kwanaki 100 ana ba ta kashi.