1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya soki kwamitin sulhun MDD

Abdul-raheem Hassan
November 16, 2020

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya soki kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan tsaro, ya kuma bukaci kasashen Turai su san ciwon kansu.

https://p.dw.com/p/3lLOK
Präsident Macron im TV zur Corona-Krise
Hoto: Ludovic Marin/AFP

Yayin wata hira da jaridar Grand Continen a birnin Paris, Shugaba Macron ya ce lokaci ya yi da kasashen nahiyar Turai za su kare 'yancinsu. Faransa na cikin kasashe biyar masu kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kowace ke da ikon hanawa ko tabbatar da kudiri.

Amirka na amfani da ikonta wajen kare martabar Isra'ila, yayin da Rasha ke tsayuwar daka na hana kwamitin kakabawa kasar Siriya takunkumi. A baya dai kalaman Macron na ayyana kungiyar tsaro ta NATO da mushen Gizaka ya tada kura.