1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron na neman shawo kan boren matasa

Binta Aliyu Zurmi MAB
July 1, 2023

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya dage wata ziyarar aiki da zai kai Jamus domin ganawa da 'yan siyasa da suka bukaci ya sa dokar takaita zirga-zirga sakamakon zanga-zangar adawa da kashe matashi da dan sanda ya yi.

https://p.dw.com/p/4TJJz
Shugaba Macron na Faransa da Firaminista Borne da ministan cikin gida DarmaninHoto: Yves Herman/AP Photo/picture alliance

Dage ziyarar aiki ya zo ne a daidai lokacin da da aka yi jana'izar matashi mai shekaru 17 da dan sanda, Faransa ya harbe saboda kin bin umurni da aka ba shi. Amma shugaban Emmanuel Macron ya nunar da cewar doka za ta yi aiki a kan wannan dan sanda da ake zargi.

A wata sanarwar da fadar mulki ta Paris ta fidtar, ta ce shugaban zai gana da 'yan siyasa da suka bukaci saka dokar takaita zirga-zirga a manyan garuuruuwan Faransa da boren ya fi kamari. Sannan zai gana da wasu magadan gari a kokarin yayyafa wa wutar rikicin ruwan sanyi.

Tun bayan da al'umma suka fantsama a kan tituna biyo bayan bindige wannan matashin, sama da jami'an kwantar da tarzoma dubu 45 ne aka baza a fadin Faransa yayin da aka kama fararen hula sama da 1300.