1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na neman hadin kai a Mali

Abdul-raheem Hassan
May 31, 2021

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce sojojinsa sun yi kadan su yaki ta'addanci a yankin Sahel tare da seta dimukuradiyya a kasar Mali.

https://p.dw.com/p/3uF4K
Südafrika Präsident Emmanuel Macron Besuch in Südafrika
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Da yake magana a taronsa na karshe da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke shirin barin gado a watan Satumba, Macron ya ce Faransa za ta sa ido sosai a Mali don ganin kasar ta koma tafarkin dimukuradiyya bayan juyin mulki na biyu cikin watanni Tara.

Faransa ta kuma gargadi sojojin da suka saka yi juyin mulki na biyu a Malin cewa, wajibi su mutunta lokacin da aka tsara na sake gudanar da zabe a 2022. Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da kungiyar ECOWAS ta dakatar da kasar Mali yayin wani taron gaggawa a kasar Ghana.