1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa da Birtaniya za su tunkari matsalar 'yan ci-rani

October 28, 2022

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da sabon firaministan Birtaniya Rishi Sunak sun tattauna batun 'yan ci-rani da ke shawagi tsakanin kasashen biyu a cikin ruwayen nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/4Io9u
Frankreich Ansprache vom Präsident Macron im Fernsehen
Hoto: Ludovic Marin/AFP

Wannan na daga cikin abubuwan da shugabannin biyu suka yi magana a kai a yayin tattaunawar farko ta wayar tarho da suka yi tun bayan da Sunak ya karbi ragamar jagorancin gwamnatin Birtaniya. Kazalika Macron da Sunak sun amince sun yi tattaunawar gaba-da-gaba a wani lokaci a shekara mai zuwa.

Danganta tsakanin Faransa da Birtaniya ta yi tsami a 'yan shekarun nan, inda galibi kasashen kan nuna wa juna dan yatsa a bisa matsalolin da suka biyo bayan ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai da ma batun 'yan ci-rani da ke zirga-zirga cikin sirri ta kogin da ya hade kasashen biyu.