1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Zaben Faransa zagaye na biyu zai yi zafi

Abdoulaye Mamane Amadou
April 11, 2022

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen sun fara gangamin yakin neman zabe zagaye na biyu, bayan da aka kasa samun wanda ya lashe zaben a zagayen farko.

https://p.dw.com/p/49kjb
Frankreich | Erste Runde der Präsidentschaftswahlen 2022 | Marine Le Pen und Emmanuel Macron
Hoto: Paulo Amorim/IMAGO

Shugaba Macron da ya samu kaso 28 cikin dari a gaban abokiyar hamayyarsa Le Pen ta jam'iyyar masu ra'ayin rikau, ya bayyana a wani taron gangami jim kadan bayan fitar da sakamakon inda yace a shirye yake ya bullo da hanyoyin kara hadin kan 'yan kasa ta kowane fanni yana mai cewa:

"Ina kira ga 'yan kasa daga kowane bangare da ma kowane matsayi suka nuna a zagayen farko da su mara mana baya, wasu na san za su yi hakan ne ba wai don na gabatar da wani tsari da ya dace da ra'ayinsu ba, amma za su yi hakan ne don hana masu ra'ayin kyamar baki cimma burinsu."

Sai dai a nata bangare 'yar takara Marine Le Pen ta yi kira ga wadanda ba su kada wa shugaba Macron kuri'arsu ba da su zabeta a zagaye na biyu na zaben da ke tafe.

A ranar 24 ga wannan watan ne dai za a fafata a tsakanin Le Pen da Macron, wanda wannan ne karo na biyu a tarihi da 'yan takarar biyu za su fafata a zaben shugabancin kasar, sai dai manazarta na ganin a wannan karon takarar za ta fi zafi fiye da a shekarar 2017.