1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Faransa: Macron da Le Pen a zagaye na biyu

Lisa Louis zMA
April 11, 2022

Masana harkokin siyasa a Faransa sun ce Le Pen mai ra'ayin mazan na iya Samun nasara a zaben shugaban kasar, sai dai kuma 'yan siyasar na iya gameta kai.

https://p.dw.com/p/49ma8
Frankreich | Erste Runde der Präsidentschaftswahlen 2022 | Marine Le Pen und Emmanuel Macron
Hoto: JB Autissier/PanoramiC/IMAGO

Duk da yake wannan na iya zama kamar sake yin zagaye na biyu na zaben 2017, lamarin ba haka yake ba. Shekaru biyar da suka gabata, yayin da masu sa ido na kasa da kasa ke fargabar nasarar Le Pen, manazarta harkokin siyasar Faransar sun yi watsi da hakan. Wannan shi ne ra'ayin Lisa Louis ta DW a birnin Paris cikin sharhin da ta rubuta kan zaben Faransa.

'Yan siyasar Faransa za su iya yin kangi wa Le Pen mai kyamar baki

Frankreich | Erste Runde der Präsidentschaftswahlen 2022 | Marine Le Pen
Hoto: Lewis Joly/AP/picture alliance

Ta yaya hakan ya faru, musamman bayan da kuri'un ra'ayin jama'a ta yi hasashen Macron zai yi nasara cikin kwanciyar hankali? Kididdigar yiwuwar nasararsa ta karu bayan da Rasha ta mamaye Ukraine saboda bisa al'ada Faransawa na marawa shugabansu baya a lokutan rikici. Amma nan take wannan tasirin ya ragu.Yayin da kasashen yamma suka sanya takunkumi kan Rasha, farashin gida ya kara karuwa, kuma babbar damuwar ita ce, yadda rayuwa za ta kasance. Da alama Le Pen ta magance wannan damuwar. Ta yi yawo cikin kananan kauyuka da garuruwa da kasuwanni tsawon watanni, tana taka rawar 'yar takara mai kusanci da jama'a. Kuma tana gaya wa kowa cewa, da zarar an zabeta, za ta ci gaba da daidaita farashin kayayyaki masu mahimmanci da rage yawan kudaden haraji gwamnati a kan man fetur da makamashi da dangoginsu. Macron, a daya hannun, ya yi jira har zuwa lokaci na karshe don shiga yakin neman zabe. Bisa dukkan alamu hankalinsa ya koma kan matsalar shugaban Rasha Vladimir Putin. Yakin neman zabensa dai 'yan kalilan ne kuma wadanda suka halarta ba su da yawa da babban taro sau daya kacal. Masu kada kuri'a na masu ra'ayin cewar, shugaban nasu bai damu da rayuwarsu ta yau da kullun ba kuma yana da tabbacin zai samu nasara.Wannan ya taimaka wa Le Pen samun nasara gagaruma da kuma dan jaridar da ya rikide zuwa dan siyasa mai ra'ayin mazan jiya-mai son tsayawa takara Eric Zemmour. Wanda ya rika yakin neman zabe da taken nuna wariyar launin fata da ya tsanata fiye da Le Pen. Hakan dai ya tunzura shi a rumfunan zabe na dan wani lokaci, har ma gaba da Le Pen. Amma sai matsayin nashi ya sauya, bayan da ya shakku dangane da tallafa wa wajen daukar 'yan gudun hijirar Ukraine tare da ci gaba da nuna rashin fahimta game da Putin, wanda ya ke sha'awa a baya.Abin mamaki, yakin neman zaben Le Pen bai samu cikas ba duk da tarihin kusancinta da Putin da kuma tallafin kudi da ta samu a baya daga Rasha. Maimakaon haka sai ya ma kara karfafata. Sannu a hankali kalmomin Zemmour sun tabbatar da ita a matsayin 'yar takara mai sassaucin ra'ayi na masu kyamar baki.

Putin na goyon bayan Le Pen a zaben shugaban kasar Faransa

Frankreich | Erste Runde der Präsidentschaftswahlen 2022 | Marine Le Pen und Emmanuel Macron
Hoto: Paulo Amorim/IMAGO

To sai dai fa hanzari ba gudu ba, 'yar shekaru 53 da haihuwar har yanzu tana da tushe sosai da wanda ya kafa jam'iyyar, mahaifinta Jean-Marie Le Pen, wanda aka yanke masa hukunci sau da yawa saboda raina kisan kiyashin da ak wa Yahudawa da kuma ingiza da kiyayyar launin fata. A matsayinta na shugabar kasa, Le Pen za ta gudanar da zaben raba gardama don sanya abin da ake kira ka'idar fifita kasa a cikin kundin tsarin mulkin Faransa. Mutanen da ke da takardar shaidar zama 'yan kasar Faransa za su sami fifiko a kan baki idan ana batun samun ayyuka, gidaje ko kula da lafiya. Watau za a  halatta wariya.Duk da yake duk abin da ya bambanta da manufofin Macron na goyon bayan Turai, duk da haka bai tsira ba domin Faransawa sun soki shi manufofin sauye-sauyen da ya shafi kasuwa wanda ke nuna fifiko ga manyan 'yan kasuwa, wanda ya bashi matsayin "shugaban masu arziki." Ya ma ayyan cewar idan ya samu zarcewa, zai kara shekarun ritaya da tilasta masu cin gajiyar gwamnati su samu horaswa ta samun aikin yi.Duk da sukar da ake yi wa Macron, ko kusa ba za a kwatantashi da barazanar da nasarar Le Pen za ta haifar ga tushen demokradiyyar Faransa ba.Hanya daya tilo da za a kare kasar daga mulkin kama-karya, ita ce a hana ta hawea karagar mulki. Ya kamata Faransawa su tambayi kansu kan yadda suke mutukar mutunta dimokuradiyyarsu, kafin su yanke shawararsu cikin makonni biyu.