1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a harin bam a Mogadishu

Zulaiha Abubakar
August 5, 2018

Kungiyar Al-shabaab ta dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda mutane gwammai suka mutu yayin da dama suka jikkata.

https://p.dw.com/p/32ecN
Somalia Anschlag in Mogadischu
Hoto: Reuters/F. Omar

Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu ciki kuwa har da jami'an 'yan sanda hudu yayin da wata mota makare da bama-bamai ta yi bindiga a Afgoye da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya,  kamar yadda hukumar 'yan sandan kasar ta sanar a ranar Lahadi. Sanarwar ta kara da cewar wasu mutane 14 da ke kusa da gurin da al'amarin ya faru na kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.

Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shaabab ta dauki nauyin wannan hari.. Kasar Somaliya dai na ci-gaba da fuskantar rashin tsaro tun daga lokacin da kungiyar Al-shabaab ta sanar da kudirinta na kau da gwamnatin kasar wacce ke da goyon bayan kasashen waje .