1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin Aljeriya da Mali

Abdourahamane Hassane
December 21, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Mali ta gayyaci jakadan Aljeriya a birnin Bamako, saboda wani abin da ta kira katsalanda da ya yi wa kasar.

https://p.dw.com/p/4aRRP
 Assimi Goita na Mali da shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboun
Assimi Goita na Mali da shugaban Aljeriya Abdelmadjid TebbounHoto: Xinhua/Filippo Attili /ANSA/IMAGO

 Hukumomin Malinsun ce jakadin na Aljeriya ya tattauna da   wakilan kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawa ba tare da saninsu ba. Aljeriya dai na shiga tsakani don dawo da zaman lafiya a arewacin Mali bayan wata yarjejeniya da aka rattabawa hannu a shekara ta 2015  tsakanin gwamnatin Mali da kungiyoyin masu dauke da makamai na Abzinawa wacce aka sanni da yarjejeniyar Algers.Tun a karshen watan Agustan da ya gabata , tashin hankali ya barke a arewacin Malin tsakanin dakarun gwamnati da na kungiyar yan tawayen abzinawa   bayan shafe shekaru takwas na kwanciyar hankali.