1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ma'aikatan filin jiragen saman Kenya sun shiga yajin aiki

September 11, 2024

An samu hargitsi a filin jiragen saman Jomo Kenyatta na birnin Nairobi da ke kasar Kenya, sakamakon matakin hukumomin kasar na bada lamunin filin jirgin ga wani kamfanin Indiya na tsawon shekaru 30.

https://p.dw.com/p/4kUWd
Filin jiragen saman Jomo Kenyatta a Nairobi na kasar Kenya da al'amura suka tsaya cak! sakamakon yajin aikin ma'aikata
Filin jiragen saman Jomo Kenyatta a Nairobi na kasar Kenya da al'amura suka tsaya cak! sakamakon yajin aikin ma'aikataHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa komai ya tsaya cak a filin jiragen saman Kenyatta da ke birnin Nairobi, inda ake dakon sanarwar da hukumomin kasar za su fitar kan wannan takaddama. Tuni dai gamayyar kungiyoyin ma'aikatan filin jiragen na Jomo Kenyatta suka fitar da sanarwar tafiya yajin aiki a shafinsu na X.

Karin bayani: Gobara a filin saukan jiragen saman Kenya

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda daruruwan matafiya da jakakkunansu ke tsaye carko-carko a filin jiragen na Nairobi, yayin da wasu ke kauracewa filin jirgin domin gudun abin da ka je ya zo.

Karin bayani: Kenya: Cin hanci ya addabi tashoshin jiragen ruwa

Matakin yajin aikin ya biyo bayan yarjejeniyar da hukumomin Kenyan suka rattaba hannu da wani kamfanin Indiya na Adani Group, wanda ya zuba hannun jarin Dalar Amurka biliyan $1.85 domin ci gaba da gudanar da filin jiragen saman na tsawon shekaru 30, matakin da ya haifar da cece-kuce a kasar ta Kenya.