1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burtaniya: binkice kan kisan jarirai

August 18, 2023

Gwamnatin Burtaniya ta bayar da umarnin gudanar da bincike bayan kama wata ma'aikaciyar jinya da laifin kisan jarirai bakwai.

https://p.dw.com/p/4VL8p
Hoto: Ruth Tomlinson/robertharding/picture alliance

Gwamnatin Birtaniya ta bayar da umarnin gudanar da binciken ne bayan da wata kotun kasar ta yanke wa ma'aikaciyar jinyar hukuncin dauri, sakamakon amsa laifin da ta yi na kisan jarirai bakwai da aka haifa da larurar rashin kosawar wasu sassan jikinsu, da kuma yunkurin kisan wasu jarirai shida a asibitin da take aiki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Birtaniyan ta ce binkice da za a gudanar zai mayar da hankali kan cikin irin yanayin da ma'aikaciyar mai suna Lucy Letby  ta aikata wannan danyen aiki a asibitin Countess of Chester da ke Arewa maso Yammacin kasar.

Ana dai sa ran binciken da za a gudanar zai samar da amsoshin da iyayen wadannan jarirai ke bukata, domin rage musu kaifin damuwa da kuma radadin wannan al'amari da ya saka su cikin kaduwa.

A wannan Jumma'a ne aka gurfanar da Lucy Letby mai shekaru 33 da haihuwa a gaban kotun birnin Manchester, inda ta amsa laifin kisan wadanda ta aikata tsakanin watan Yunin shekara ta 2015 zuwa Yunin shekara ta 2016.