1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban hukumar kwallon kafa na Spain ya sauka

Abdourahamane Hassane
September 11, 2023

Shugaban hukumar kwallon kafa na Spain Luis Rubiales, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa

https://p.dw.com/p/4WCcW
Luis Rubiales Shugaban hukumar kwallon kafa na Spain
Luis Rubiales Shugaban hukumar kwallon kafa na Spain Hoto: Denis Balibouse/REUTERS

Luis Rubiales na son kuma  ya sallama ga barin mukaminsa na mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar na Turai wato UEFA. Hakan kuwa ya biyo bayan kai da kawon da ake yi da shi a gaban kotu saboda karar da yar wasan kwallon kafa na mata ta Spain Jennifer Hermoso ta shigar a gaban kotun a makon jiya. Wadda a wajen bikin karramawar yan wasan na spain da suka ci kofin duniya na mata a watan da ya gabata ya sumbaceta a baki ba tare da ta so ba.

 Luis Rubiales tare da Jennifer Hermoso
Luis Rubiales tare da Jennifer HermosoHoto: RFEF/Kim Price/Zuma/picture alliance