1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Liverpool ta casa Barcelona a kofin zakarun Turai

Gazali Abdou Tasawa
May 8, 2019

A wasannin cin kofin kwallon kafa na zakarun Turai, kogo ya juye da mujiya a daren jiya inda kungiyar Liverpool ta Ingila ta casa kungiyar Barcelona ta Spain da ci hudu da babu a wasan zagaye na biyu na kusa da na karshe

https://p.dw.com/p/3I7E3
Fussball Champions League Halbfinale l FC Liverpool vs FC Barcelona
Hoto: Reuters/P. Noble

A wasannin cin kofin kwallon kafa na zakarun Turai, kogo ya juye da mujiya a daren jiya inda kungiyar Liverpool ta Ingila ta casa Kungiyar Barcelona ta kasar Spain da ci hudu da babu a wasan zagaye na biyu na kusa da na karshe da aka buga a daren jiya a filin wasa na Anfield. 

A makon da ya gabata a wasan zagayen farko a filin wasa na Noucamp, kungiyar Barcelona ta doke Liverpool da ci uku da babu, amma kuma a daren jiya Liverpool ta rama wa kura aniyarta har da dori inda ta doke ta da ci hudu ba nema. Jurgen Klupp shi ne mai horas da 'yan wasan kungiyar ta Liverpool. 'Yan wasa Divock Origi da Georgino Wajnaldum ne suka ci wa kungiyar ta Liverpool kwallayen guda hudu wato kowane biyu-biyu.


Wannan nasara ta bai wa kungiyar ta Liverpool damar kaiwa karo biyu a jere wasan karshe na cin kofin zakarun Turai inda za ta fafata da kungiyar da za ta yi nasara a karawar da za a yi a wannan Laraba tsakanin Kungiyar Tottenham da kuma Ajax wacce ta doke Tottenham din a gidanta da ci daya mai ban hanci a makon da ya gabata.