1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin dakarun Haftar a Libiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 22, 2020

Sabon rikici na shirin kunno kai a kasar Libiya, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 10 tsakanin bangarorin da ke yakar Juna.

https://p.dw.com/p/3WfBs
Libyen zerstörtes Gebäude in Tripoli
Sababbin hare-hare a Libiya bayancimma yarjejeniyar tsagaita wutaHoto: Imago

Rahotanni daga kasar Libiya na nuni da cewa sojojin da ke marawa babban janar din sojan kasar da ke rike da wasu yankuna na Libiyan janar Khalifa Haftar sun kai wasu jerin hare-hare da rokoki a babban birnin kasar da ke karkashin ikon gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita. Gwamnatin Libiyan dai da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Dunyar, ta ce hare-haren ya saba da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 10 da aka cimma tsakanin Rasha da Turkiyya da ke marawa bangarorin da ke yakar juna a Libiyan baya.