Libiya ta saki jami'an kotun ICC
July 2, 2012Tsoffin 'yan tawayen Libiya sun ba da sanrwar sakin jami'an kotun hukunta miyagn laifuka ta kasa da kasa(ICC) da aka tsare a wannan kasa. Ajami Al Atiri, komamdan sojojin da ke tsare da dan Gadhafi, Saif al Islam shine ya ba kafafen yada labaru sanarwar daukar wannan mataki a birnin Zintan. Ya ce nan ba da jimawa ba jami'an za su fice daga kasar. Su dai jamian kotun su hudu da suka hada da Melinda Taylor wadda lauya ce daga kasar Australiya kusan makonnii uku kenan da aka tsare su a Libiya bayan da suka kai wa Saif al Islam ziyara. Kasar ta Libiya tana zarginsu ne da ba Saif al Islam wani bairo mai hade da kyamara da kuma wata wasika daga Mohammed Ismail wanda dan hannun dama ne na iyalin Gadhafi.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman