1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya na fuskantar koma baya a siyasance

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 23, 2022

Babban zaben da aka shirya gudanarwa a watan Yuni, shi ne ake fatan zai dora kasar kan tafarkin dimukuradiyya mai dorewa kasancewar ya sami amincewar Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai kuma har yanzu babu tabbas

https://p.dw.com/p/48viU
Firaministoci biyu na Libya Fathi Bashagha da Abdul Hamid Mohammed Dbeibah
Internationale Libyen Konferenz
Babban taron kasa da kasa kan LibyaHoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

Ana dai iya cewa Libiyan ta koma tamkar lokacin da ake tsaka da yakin basasa a kasar, gabanin watan Fabrairun 2021 da wakilan mayakan da ke gaba da juna suka amince da kafa gwamnatin rikon kwarya. Sun dai kai wannan matsayi ne da tallafin Majalisar Dinkin Duniya, inda a wancan lokaci suka amince da Abdul Hamid Dbeiba a matsayin firaministan rikon kwarya. An dai tsara cewa gwamanatin ta Dbeiba za ta shirya babban zabe domin mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya, sai dai zaben na watan Disambar bara bai yiwu ba. Abin tambayar shi ne, a ina matsalar take? A hirarsa da tashar DW, Thomas Volk jami'in da ke kula da Libiya a gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ya yi tsokaci.
"Yace a daidai wannan lokaci, tabbas yakin da ake a Ukraine na shafar Libiya, ba wai kawai domin Libiya ta dogara da Rasha wajen samun alkama ba, yadda farashin kayan abinci ke yin tashin gauron zabi, tabbas zai yi mummunan tasiri a kan al'ummar kasar. Ba ya ga haka kuma, sakamakon mamayar da Rasha ta yi a Ukraine, hankalin duniya ya koma Ukraine musamman bangaren dangantakar kasa da kasa da kuma fannin tsaro. Hakan ya bai wa Turkiyya dama ta kara samun karfi a Libiya, kuma akwai yiwuwar ta mara wa Dbeiba baya. Turkiyya na kan hanyar kara karfin tasirin da take da shi a Libiya."

Internationale Libyen Konferenz
Taron kasa da kasa kan LibyaHoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

Sai dai duk wannan matsalar ka iya sauyawa ta hanyar yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, a cewar Hager Ali kwararriya a kan al'amuran siyasa kana mai bincike a kan siyasar kasashen Larabawa a cibiyar nazari kan al'amuran kasa da kasa ta Jamus GIGA da ke birnin Hamburg. Sai dai a ganinta ko da wajen yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima ma, ana iya samun matsala tana mai cewa:

"Tabbas za ka iya sauya dokokin zabe ta yadda za su ba ka damar cin zabe ko hana abokan hamyyarka yin katabus. Haka kuma kana iya yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta yadda zai ba ka duk wata dama da kake bukata. Ina iya cewa siyasar da ake a ciki a kasar, musamman ta fuskar albarkatun kasa ka iya taka rawa. Ya danganta da yadda ake tafiyar da albarkatun da kasar ke da su, wanda hakan ka iya bai wa wasu manyan 'yan siyasa damarmaki. Akwai rijiyoyin man fetur a kudanci da arewacin Libiya, kuma daga nan ne 'yan siyasar za su nuna karfin rawar da suke iya takawa. Ana ganin cewa mafi yawancin rijiyoyin man fetur din a yanki daya suke kawai, ta yadda mutum zai iya daukar nauyin kansa da su." 

Al'amura dai sun fara tabarbarewa a Libiya, bayan da a ranar 10 ga watan Fabrairun da ya gabata. 'Yan majalisar kasar a Tobruk da ke yankin Arewa maso gabashi, suka zabi Fathi Baschaga da ya kasance tsohon ministan cikin gidan na Libiyan a matsayin firaminista na biyu. A cewarsu sun zabe shi kasancewar wa'adin Firaminista Abdul Hamid Dbeiba da aka nada da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a watan Fabrairun bara, ya kare tun cikin watan Disamba da aka shirya gudanar da zabe. Sai dai kuma a wani abu mai kama da son kai cikin wannan wata na Maris, Dbeiba ya bayyana cewa zai ci gaba da rike madafun iko tare da yin biris da abin da ke faruwa a yankin Arewa maso gabashin kasar.