1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori dakarun Haftar daga sansanin sojin sama

Binta Aliyu Zurmi
May 18, 2020

Dakarun gwamnatin kasar Libiya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya sun sanar da karbe ikon wani sasnsanin sojin sama da ke wajen Tripoli daga hannun abokan hamayyarsu masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar.

https://p.dw.com/p/3cPd0
Libyen Regierungssoldaten
Hoto: picture-alliance/AA/H. Turkia

Col. Mohammed Gnounou da ke magana da yawun gwamnatin kasar ta Libiya ne ya tabbatar da wannan nasara ta karbe sansanin sojin sama na al-waitya da ke kudu maso yammacin kasar. Tuni Firai Ministan kasar ya sanar da cewa sannu a hankali za su karbe dukka garuruwan da ma yankunan da ke hannun dakarun Janar Haftar din.

Za a iya cewa wannan wani babban komabaya ne ga Khalifa Haftar da ma dakarunsa da suka kwashe sama da shekara suna ikirarin sai sun karbe ikon birnin Tripoli.