1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Harin martani a Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 1, 2022

Ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa harin da Rasha ta kai kan tashar makamashin Ukraine, ta kai shi ne da nufin mayar da martani kan barazanar da ake mata.

https://p.dw.com/p/4KLXR
Russischer Außenminister Sergej Lawrow
Hoto: Vitaliy Belousov/SNA/imago

Ministan harkokin kasashen ketaren na Rasha Sergei Lavrov ya bayyana hakan ne, a wata hira da ya yi da manema labarai da aka nuna ta kafar talabijin din kasar. Ya kara da cewa, tashar makamashin na bayar da gudunmawa wajen karfafa sojojin Ukraine. A cewarsa, sun kai harin ne domin rage adadin fararen hular da yakin kasashen biyu ke ritsawa da su. Haka kuma Lavrov ya yi zargin cewa, kungiyar tsaro ta NATO da Amirka ma na amfani da irin wadannan dabarun yakin a baya-bayan nan.