Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai
May 30, 2022A karshen makon da ya gabata, aka kawo karshen wasannin zakarun na Turai da wasan karshen karshe a tsakanin Kungiyar Real Madrid ta Spaniya da Liverpool daga Ingila, inda a mintoci na 59 dan wasa Vinicius Junior na Real Madrid kuma dan kasar Brazil ya jefa kwallo a ragar Liverpool a filin wasa na Stade de France da ke birnin Paris a gaban dubban 'yan kallo gami da wasu milyoyi a fadin duniya da suka kalli wasan kai tsaye a daren Asabar agogon kasashen Turai. Wannan kwallo tilo da Vinicius Junior ya jefa ya tabbatar da nasara karo na 14 ga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Wannan wasan karshe a tsakanin Kungiyar Real Madrid ta Spaniya da Kungiyar Liverpool daga Ingila, ya bar baya da kura inda magoyan bayan Liverpool suka yi zargin 'yan sandan birnin Paris, inda aka gudanar da wasan, da cewa sun musguna musu lokacin da suke kokarin shiga filin wasa, lamarin da ya kai ga saka hayaki mai saka hawaye. Sai dai 'yan sanda sun ce wasu magoya bayan Liverpool sun yi yunkurin shiga da tikiti na jebu abin da ya janyo hatsaniyar. Tuni mahukunta Birtaniya suka bukaci gudanar da bincike domin sanin gaskiyar abin da ya faru.
Christopher Nkunku na Kungiyar Leipzig da ke nan Jamus, ya fara tunanin komawa kungiyar kwallon kafa ta Paris-Saint-Germain da ke Faransa. A matsayin dan matasa a shekara ta 2010 Nkunku ya fara wasa da kungiyar ta Paris Saint-Germain, har zuwa shekara ta 2019 lokaci da ya koma Leipzig da ke Jamus. Karkashin yarjejeniyar, Nkunku ya zauna a Leipzig har zuwa shekara ta 2024 amma yanzu Paris Saint-Germain tana neman ya koma, inda rahotanni ke cewa akwai kuma kungyoyin da ke zawarcin dan wasan.
Yayin da ake ci gaba da shirye-shirye wasan neman cin kofin kwallon kafa ta duniya a karshen wannan shekara da kasar Katar za ta dauki nauyi, kasashen Afirka da suka samu damar shiga gasar suna ci gaba da shirye-shiryen kamar sauran takwarorinsu na duniya. Alhaji Sani Ahmed Toro tsohon sakataren hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya kana tsohon kwamishinan wasanni a jihar Bauchi ya bayar da wasu shawarwari ga kasashen da za su wakilci Afirka.
A birnin Paris na Faransa ana ci gaba da fafatwa kan wasan Tennis mai tasiri na shekara-shekara da ake kira Roland Garros, kuma a ranar Talata mai zuwa ake fafata wasan kusa da na karshe tsakanin Novak Djokovic da Rafael Nadal.